in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin sayar da kayayyaki a sassan duniya fiye da 180 sun shiga birnin Shanghai
2017-01-09 11:31:47 cri
Bisa kididdigar da kwamitin harkokin cinikayya na birnin Shanghai na kasar Sin ya yi, ya zuwa karshen shekarar 2016, a cikin kamfanonin sayar da kayayyaki a sassan duniya 340, fiye da guda 180 sun bude rassa a birnin Shanghai na kasar Sin, wanda hakan ke nuna cewa birnin na biye da birnin London da Dubai a matsayi na uku a duniya a wannan fanni.

Yanzu haka dai birnin Shanghai yana daya daga cikin biranen da suka fi bude kofa a fannin cinikayya a duniya. An ce a halin yanzu, a kalla kan ko wane mutane 3400 akwai kantin sayar da kaya daya a birnin, wanda hakan ke nuna yawansu ya kai matsayi na koli a kasar Sin a sha'anin sayar da kayayyaki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China