Cikin wata sanarwa da tawagar ta UNSOM ta fitar a ranar Asabar tace, Conway zai maye gurbin Peter de Clercq dan kasar Netherlands, wanda sakatare janar na MDDr yayi matukar yawawa da irin sadaukarwar da ya nuna a lokacin wa'adin aikinsa a kasar Somalia.
Conway mai shekaru 49 a duniya, ya samu digirinsa na biyu a fannin fasaha daga jami'ar Carleton da kuma jami'ar Western Ontario, da kuma digirinsa na farko daga jami'ar Winnipeg.
Jami'in dan kasar Kanada ya samu kwarewar aiki mai yawa kuma ya shafe shekaru masu yawa yana aiki karkashin MDD, kuma ya rike mukamai masu yawa a kasar Sudan ta kudu, inji sanarwar. (Ahmad)