A wannan rana da safe, aka tayar da bom da aka ajiye a cikin wata mota a gaban kofar ma'aikatar 'yan kwadagon dake Mogadishu, babban birnin kasar, daga baya dakaru masu dauke da makamai sun kutsa cikin babban ginin ma'aikatar, har suka yi musayar wuta da jami'an tsaron kasar ta Somaliya. Mataimakin ministan 'yan kwadagon kasar Saqar Ibrahim Abdalla ya rasa ransa sakamakon lamarin.
Daga bisani kungiyar Al-Qaida a Somaliya ta sanar da daukar alhakin kai harin. (Bilkisu)