Abdulkadir Abdirahman, daraktan Aamin Ambulance, wato bangaren dake bada hidimar daukar marasa lafiya kyauta a Mogadishu, ta tabbatarwa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa an samu karuwar mutanen da suka rasu a harin, sannan wadanda suka ji raunuka suna samun kulawar likitoci a asibiti.
Wata mota makare da ababen fashewa ta afka kan wani shahararren gidan sayar da abinci dake kan titin Makka Al-Mukarrama, lamarin da ya haifar da lalacewar gine ginen dake daura da wajen.
Shaidun gani da ido sunce harin bom din yayi muni matuka. "Ina kusa da wajen a daidai lokacin da motar dauke da bom ta kutsa ginin. Naga gawarwakin mutane a warwatse a yankin kuma tagogi sun tarwatse," Ise Awil, wani da ya ganewa idonsa ya tabbatarwa Xinhua.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin kawo yanzu, amma kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabab ta sha daukar alhakin makamancin harin a lokutan baya. (Ahmad Fagam)