in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a mahauciyar guguwar Idai a Mozambique ya karu zuwa 84
2019-03-19 11:13:37 cri

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar Mozambique (INGC) ta sanar a jiya Litinin cewa, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ya karu zuwa 84, kana wasu mutane 1,500 sun jikkata.

Ita dai mahaukaciyar guguwar ta Idai ta haifar da mummunar barna a lardunan Sofala, Manica da Zambezia dake tsakiyar Mozambique da kuma lardin Inhambane dake arewacin kasar a daren ranar Alhamis, inda ta yi sanadiyyar ambaliyar ruwa a wasu kauyuka da garuruwa, lamarin da ya sa dubban iyalai suka rasa gidajensu.

Darakta janar na hukumar INGC Augusta Maita, ya fadawa taron manema labarai a Maputo cewa, gwamnati ta samar da kudade kusan dala miliyan biyar da kuma karin dala miliyan 1.5 daga masu bada gudunmowa na kasashen waje inda aka yi amfani da kudaden wajen samar da kayayyakin jin kai, da kayayyakin bukatu ga mutanen da ibtila'in ya shafa.(Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China