in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar bada taimako ta Sin ta mika gudummawa ga kasar Mozambique
2019-03-28 10:51:05 cri

Tawagar bada taimako ta kasar Sin ta gudanar da ayyukan jin kai a birnin Beira dake kasar Mozambique wanda yake fama da bala'in mahaukaciyar guguwa mai suna "Idai" a ranar 26 ga wata.

An gudanar da taron kula da majinyata wanda hukumar kula da harkokin jin kai ta MDD ke jagoranta a cibiyar bada umurni ta birnin Beira a ranar 26 ga wata, inda ma'aikatar harkokin kiwon lafiya ta kasar Mozambique ta mika ayyukan bada jinya da ceton mutane ga tawagar kasar Sin.

Ministan kula da aikin noma da tsaron hatsi na kasar Mozambique da sauran jami'an gwamnatin kasar sun gana da shugaban tawagar bada taimako ta kasar Sin, inda suka una godiya ga kasar Sin domin ta tura tawaga zuwa kasar Mozambique don bada gudummawa, kana sun bayyana bukatunsu ga tawagar Sin a fannonin kiwon lafiya, da magance cututtuka, da yin jigilar kayayyaki da dai sauransu.

Tawagar bada taimako ta kasar Sin tana fatan za ta iya gudanar da ayyukansu bisa goyon bayan gwamnatin kasar Mozambique don samar da taimako yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China