Shugaban tawagar Chen Liping ya bayyana cewa, sharadin bada agajin kiwon lafiya na kasar Mozambique yana da koma baya, kuma akwai karancin kayayyakin aikin likitanci sosai, don haka 'yan tawagar sun hada kai sosai tare da likitocin wurin wajen sabunta tunaninsu wajen aikin, da kyautata kwarewarsu wajen gudanar da aikin.
Bisa kididdigar aka bayar, an ce, a cikin shekaru biyu da suka gabata, tawagar bada agajin jiyya ta kasar Sin ta sa hannu a cikin tiyata 2024, da sanya maganin kashe zafin ciwo ga majinyata 3151, da bada ceton gaggawa ga mutane 118, da yiwa mutane kusan dubu 10 allurar gargajiyar Sin. Banda wannan kuma, gwargwadon karfinta, tawagar bada jinya ta Sin ta bada aikin hidimar likitanci da horaswa ga mazauna wurin da Sinawa dake zaune a kasar, baya ga samar da jiyyar kyauta fiye da sau 10.
A watan Disamban bara, ministan kiwon lafiyar kasar Mozambique ya bada lambar yabo ga dukkan mambobin tawagar bisa kwazon da suka nuna.(Kande Gao)