"Jaddada manufar inganta rayuwar bil adama da kyautata yin cudanya karkashin shawarar ta BRI yayi matukar dacewar da manufofin MDD. Mun yi murna matuka kuma a shirye muke mu yi hadin gwiwa ta kowace fuska," Grandi ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen taron dandalin kasashen Asiya na Boao ko kuma (BFA), wanda ke gudana a yankin tsibirin kudancin kasar Sin dake lardin Hainan.
Shawarar ta ziri daya da hanya daya, wadda aka gabatar da ita a shekarar 2013, da nufin gina tsarin cinikayya da aikin samar da kayayyakin more rayuwa wanda zai hade nahiyar Asiya, Turai, da Afrika, wanza ya zarta hanyar siliki ta kan teku mai dadden tarihi.
Shawarar tana kara samun karbuwa kuma tana kara samun sabbin bangarorin duniya dake burin shiga hadin gwiwar, inji Grandi, ya jaddada cewa manufar kafa shawarar ta BRI tana da matukar muhimmanci ga hukumarsa kasancewar zata yi matukar bada gudunmowa ga cigaban aikin kula da 'yan gudun hijira na kasa da kasa.(Ahmad Fagam)