in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta damu game da halin da wani gungun jama'a ke ciki a kan iyakar Algeria da Nijar
2019-01-04 12:48:44 cri
Hukumar MDD mai lura da harkokin 'yan gudun hijira ko UNHCR a takaice, ta ce ta damu da halin da wasu gungun jama'a ke ciki, bayan da suka isa a kan iyakar Algeria da Jamhuriyar Nijar

Hukumar ta UNHCR ta bayyana a jiya Alhamis cewa, cikin gungun jama'ar akwai wadanda ka iya fadawa wani mawuyacin hali, kuma mafi yawancinsu sun fito ne daga kasashen Syria, da Yemen da kuma Falasdinu.

Cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce ta samu wasu bayanai dake nuna cewa, gungun mutanen na kunshe ne da mutum 120, wadanda aka tsare a cibiyar Tamanrasset dake kudancin kasar Algeria, kafin daga bisani a kwashe su zuwa yankin Guezzam dake kan iyakar kasashen biyu a ranar 26 ga watan Disambar da ya gabata.

Sanarwar ta ce wasu daga mutanen hukumar ta UNHCR ta yi musu rajista, bayan da suka tserewa tashe tashen hankula daga yankunansu na asali, suke kuma neman mafaka a kasar Algeria karkashin tanajin dokokin kasa da kasa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China