Da yake jawabi ga kwamitin, Flippo Grandi ya gabatar da ainihin abun da duniya ke fuskanta a yanzu, inda ake samun sabbin rikice-rikice dake haifar da gudun hijira a kusan dukkan sassan duniya.
Ya bukaci kwamitin ya mara baya ga matakan kawo karshen abubuwan dake haddasa rikici.
Har ila yau, ya yi tsokaci kan batun yaki da safarar bil adama tare da ci gaba da kare 'yan gudun hijira yayin da ake kokarin shawo kan rikice-rikice.
Flippo Grandi ya ce adadin mutanen da suka tserewa matsugunansu bisa tilas a fadin duniya na tunkarar miliyan 66, adadin da ya karu daga miliyan 42 a shekarar 2009. Ya ce adadin ya kunshi 'yan gudun hijira miliyan 17.2 dake karkashin kulawar hukumarsa, inda aka samu karuwar adadin da kaso 70 cikin shekaru 8. (Fa'iza Mustapha)