in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta kaddamar da gangami mai taken "samar da tudun mun tsira mai nisan kilomita biliyan biyu" a duniya
2019-01-09 10:39:14 cri
Hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ko kuma UNHCR a takaice ta kaddamar da wani gangami a duk fadin duniya a jiya Talata, mai suna "samar da tudun mun tsira mai nisan kilomita biliyan biyu", domin fadakar da jama'a irin wahalhalun da 'yan gudun hijira suke sha ta hanyar yin sassarfa ko hawa babura. Za'a yi kokarin cimma burin yin tafiyar da ta kai tazarar kilomita biliyan biyu, domin nuna kulawa da goyon-baya ga 'yan gudun hijira dake sassa daban-daban na duniya.

A cikin wata sanarwar da ta bayar jiya, hukumar UNHCR ta ce, alkaluman da ta tattara na nuna cewa, tsawon tafiye-tafiyen da mutanen da aka tilasta musu barin muhallansu suka yi ya kai kimanin kilomita biliyan biyu a kowace shekara, a kokarin isa mafaka ko kuma tudun mun tsira.

UNHCR ta bayyana fatanta na tattara dala miliyan 15 ta hanyar shirya wannan gangami, domin ta biya kudin da 'yan gudun hijirar suke bukata, ciki har da yi musu rajista, da abinci, da wurin zama, da tallafi, da kiwon lafiya da sauransu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China