An ce, bisa makamancin lokacin bara, yawan 'yan gudun hijira da bakin haure da suka tashi daga kasar Turkiya, da nufin ratsa bahar Rom zuwa kasar Girka ya ragu da kashi 94 cikin dari, amma yawansu dake tashi daga arewacin nahiyar Afirka zuwa kasar Italiya bai sauya ba.
Rahoton ya kara da cewa, a watanni 6 na farko na shekarar bana, yawan 'yan gudun hijira da bakin haure da suka mutu yayin da suke kokarin tashi zuwa nahiyar Turai ya yi kusan daidai da na bara, inda a kalla wasu 2253 ne suka rasa rayuka yayin da suke neman tsallake bahar Rom. (Zainab)