in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kaddarorin kasar Sin suna kara samun karbuwa daga masu zuba jari na kasa da kasa
2019-03-19 16:42:32 cri
A bisa wani sabon rahoton binciken da Amurka ta yi game da manyan kaddarori na duniya ya nuna cewa, a halin yanzu, hankalin masu zuba jari na fadin duniya ya yi matukar karkata wajen nuna sha'awarsu na zuba jari a bangaren kaddarori mallakar kasar Sin nan da wasu shekaru uku masu zuwa.

Binciken na shekara shekara, mai taken "Global Fixed Income Study", ya gano cewa, kashi 58 bisa 100 na wadanda suka mallaki kaddarori a arewacin Amurka suna shirin kara zuba jarinsu a kasar Sin a cikin shekaru uku masu zuwa, kamar yadda aka bayyana rahoton binciken a ranar Litinin wanda hukumar Invesco ta gudanar, wato wani kamfani mai zaman kansa mai kula da harkokin zuba jari na Amurka.

Binciken wanda aka gudanar ta hanyar yin tattaunawar gaba da gaba a tsakanin masu zuba jari 145 daga fadin yankunan arewacin Amurka, Turai, gabas ta tsakiya, Afrika da kuma yankin Asiya da na Pasifik, wadanda su ne ke da alhakin tafiyar da harkokin zuba jarin da kimarsu ta kai dala triliyan 14.1 karkashin gudanarwar hukumar daga ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2018.

A cewar rahoton, a kokarin tabbatar da samun fadadar hanyoyin tattalin arziki da samun tagomashi, kaddarorin kasar Sin suna kara samun bunkasuwar masu zuba jari ta hanyar kasuwanci da ya shafi shiyyoyin duniya.(Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China