in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaran Sin da Italiya sun tattauna kan hadin-gwiwarsu ta fannin "ziri daya da hanya daya"
2019-03-21 10:37:01 cri

An yi shawarwari tsakanin kafofin watsa labaran kasashen Sin da Italiya mai taken "ziri daya da hanya daya da hadin-gwiwar kafofin watsa labaran Sin da Italiya" a birnin Rome, fadar mulkin kasar Italiya. Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ne ya shirya shawarwarin, tare da taimakon jaridar Economic Daily ta kasar Sin, da babban kamfanin watsa labarai na Class Editori na Italiya gami da jaridar Il Sole 24 Ore ta Italiya, al'amarin da ya zama wani muhimmin fanni na ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar.

A yayin shawarwarin, wasu kafofin watsa labaran kasar Sin, ciki har da CMG, da jaridar Economic Daily, da jaridar China Daily, da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, gami da jaridar People's Daily, sun zurfafa tattaunawa da takwarorinsu na kasar Italiya game da yadda za su fadada hadin-gwiwa karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya". Wakilan kafofin watsa labaran Italiya sun bayyana cewa, ziyarar Xi Jinping a kasar za ta sanya babban kuzari ga bunkasuwar dangantakar abota ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, kuma hadin-gwiwarsu dake kawowa juna moriya na da makoma mai haske.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China