Taron karramawar da aka gudanar da yammacin ranar Laraba, ya ba kamfanin Huawei wani dandalin na nuna sababbin fasashohinsa na sadarwa, inda suma abokan huldarsa suka bayyana irin na su dabaru kan yadda za su bunkasa kasuwancinsu a Kenya.
An bada lambobin yabo 43 ne a fannoni daban daban da suka shafi tsarukan rage cunkoson sadarwa da sarrafa bayanai da horas da abokan hulda da kwararrun masu bada gudunmuwa a bangaren .
Shugaban kamfanin Huawei a Kenya, Stone He, ya ce aiki da kamfanin Redington Gulf da sauran abokan huldarsu na Kenya a bangaren fasahar sadarwa ya ba Huawei damar kai kayayyaki da hidimomin fasahar sadarwa kasar, wanda ya taimakawa musu gaggauta samun sauyin fasahohin zaman tare da biyan bukatun kasuwancinsu. (Fa'iza Mustapha)