in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude makarantar koyon fasahohin sana'o'i na Luban na Afirka na farko a Djibouti
2019-03-29 09:34:56 cri

A jiya ne, aka bude makarantar koyon fasahohin sana'o'i na Luban na Afirka na farko a kasar Djibouti, da nufin horas da jama'a musamman matasan kasar ingantattun dabarun koyon sana'o'i.

Shugaban kasar Djibouti Isma'il Omar Guelleh da jakadan kasar Sin a Djibouti Zhou Ruisheng da shugaban kamfanin CCECC na kasar Sin Yuan Li na daga cikin mahalarta bikin bude makarantar.

A jawabinsa na bude taron, shugaba Guelleh, ya bayyana cewa, makarantar za ta taimaka wajen inganta kwarewar dalibai, da samar da muhimman ayyukan raya kasa a sassa daba-daban na kasar, da ma samarwa kasar masu basira da cikakkiyar horo.

Ya kuma kula da muhimmin kayayyakin more rayuwa da aka gina a kasar a shekarun da suka gabata, yana mai jadadda cewa, makarantar koyon sana'o'i na Luban, zai kara takarar kasar ta hanyar horas da matasan kasar masu basira, duba da yadda kasar ke bukatar sabbin fasahohin kere-kere da kara daga matsayin ci gaban tattalin arzikin kasar.

Ana sa ran makarantar wadda ita ce ta farko cikin makarantun koyon sana'o'i na Luban guda 10 da aka shirya kafa su a sassan nahiyar Afirka,zai bunkasa ci gaban kasar ta Djibouti ta hanyar horas da matasan kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China