in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara shaida yadda kasar Sin ke kara bude kofarta ga kasashen waje a Hainan
2019-03-28 20:33:47 cri
A taron dandalin tattauna harkokin Asiya da aka shirya a bara a birnin Boao na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping, ya sanar da wasu manyan matakai guda hudu, ciki har da kara fadada hanyoyin shigar da jarin waje a kasuwar Sin, da samar da muhallin zuba jari mafi jawo hankali, da karfafa kiyaye ikon mallakar fasaha, da kuma sa himma wajen shigo da kayayyaki a kasar, matakan da suka soma yunkurin bude kofar kasar ga waje na sabon zagaye.

Bayan shekara guda, a gun taron dandalin tattaunawar din na Boao na shekarar 2019, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya kara ba da jerin alamun karfafa bude kofa ga kasashen ketare. A lardin Hainan wanda ya kasance muhimmiyar taga ta kasar Sin, wajen yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare na tsawon shekaru 40, an kara shaida yadda kasar Sin ke kokarin kara bude kofarta ga kasashen waje.

A bikin bude taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da jawabi, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta gaggauta tsara dokoki, da ka'idojin da za su tallafawa dokar zuba jari ta baki, kuma hakan zai kara fadada hanyoyin shigowar jarin waje, tare kuma da kara bude kasuwar hada-hadar kudi ga baki.

Ana iya gano cewa, duk wadannan matakai suna shafar fannonin shiga kasuwar Sin, da muhallin zuba jari, da kiyaye ikon mallakar fasaha, da kuma hadin kan fasaha da dai sauransu, wadanda ke kasancewa muhimman fannonin da kasar Sin za ta dora muhimmanci a kai, a yayin da take kara bude kofa ga kasashen ketare, su ne kuma muhimman batutuwan da ke jawo hankalin masu jarin waje dake neman ci gaba a nan kasar Sin.

Kasar Sin ta ba da amsa cikin lokaci, da daukar matakai, domin biyan bukatunta na kara bude kofa ga kasashen ketare, tare kuma da amfanawa kasa da kasa wajen cin moriyar ci gabanta, kana sun nuna cewa, kasar Sin na daukar nauyin dake wuyanta game da neman ci gaban duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China