in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya jaddada fadada hanyoyin shigar jarin waje cikin kasuwar kasar Sin
2019-03-28 20:17:15 cri





Da safiyar yau Alhamis ne aka bude taron dandalin tattauna harkokin Asiya a birnin Boao na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. A bikin bude taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da jawabi, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta gaggauta tsara dokoki, da ka'idojin da za su tallafawa dokar zuba jari ta baki, kuma hakan zai kara fadada hanyoyin shigowar jarin waje, tare kuma da kara bude kasuwar hada-hadar kudi ga baki.

Taron na bana na da taken "makomar bai daya, da daukar matakai na bai daya, a kuma samun ci gaba na bai daya", wanda kuma ya samu halartar wakilai sama da 2000, da suka zo daga kasashe da shiyyoyi fiye da 60.

A jawabin da Mr. Li Keqiang ya gabatar a wannan rana, ya ce, a gaban kalubalen da ake fuskanta na dakushewar tattalin arzikin duniya, ya zama dole sassa daban daban su gano hanyar samun moriyar juna, tare kuma da kiyaye tsarin kasa da kasa da ke karkashin MDD, ya ce, "kasar Sin na son ganin a gudanar da cinikayya cikin 'yanci da adalci. Ya kamata kasa da kasa su sa kaimi wajen gyaran tsarin gudanar da harkokin duniya, sai dai gyaran ba ya nufin a kafa wani sabon tsari, ko kuma an yi shi ne domin biyan bukatun wasu kasashe kalilai, a maimakon haka, ya kamata a biya bukatun daukacin kasashe. Kasar Sin na fatan ganin an yi wa kungiyar WTO gyare-gyaren da suka wajaba, amma ya zama dole a kiyaye manyan ka'idojinta."

Li Keqiang ya kara da cewa, bude kofa ga kasashen ketare babbar manufa ce ta kasar Sin, kuma dokar zuba jari ta baki wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka, a wani kokari na samar da yanayin kasuwanci mai sauki, wanda ke da dokokin da ake bi. Ya ce, yanzu gwamnatin kasar Sin ta fara aikin tsara dokoki, da ka'idoji da za su tallafa wa dokar, domin samar da karin bayani game da dokar, ya ce, "Za mu kammala tsara wadannan dokoki, da ka'idoji kafin karshen wannan shekara. Daga ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa, za mu fara aiwatar da su, tare da dokar zuba jari ta baki. Za mu saurari ra'ayoyin bangarori daban daban, musamman ma shawarwarin da baki 'yan kasuwa suka samar, don mu inganta su."

Firaministan ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta kara fadada hanyoyin shigar jarin waje cikin kasuwarta, kuma za ta bai wa baki 'yan kasuwa dama daidai da gwargwadon takwarorinsu na gida, tare kuma da kayyade fannonin da suke iya zuba jarinsu. Kafin karshen watan Yunin bana, kasar Sin za ta sake gabatar da gyararriyar takardar jerin sassan da ake hana zuba jarin baki, da ma takardar jerin sassan da ake hana zuba jarin baki cikin su, a yankin gwajin ciniki maras shinge.

Firaministan ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga baki ta fannonin kasuwar hada-hadar kudi, da hidimomin zamani, za ta kuma ba wa kamfanonin gida da na waje dama ta bai daya. Har wa yau, za ta kara kiyaye hakkin mallakar ilmi, don kiyaye moriyar baki 'yan kasuwa. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China