Hukumar ta ce, yawan kudaden harajin da za a rage kan kayayyakin da ake shigo da su a bana, zai kai kusan Yuan biliyan 225, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 33.5. Haka kuma,tun a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2018, hukumar ta rage irin haraji da ake bugawa kayayyakin da ake shigo da su daga kaso 17 zuwa 16 cikin 100, da kuma kaso 11 cikin 100 zuwa kaso 10 cikin 100.
Bugu da kari, za a rage irin wannan haraji kan kayayyakin da ake shigo da su, daga sauran kasashe ta hanyar cinikayyar yanar gizo, domin bunkasa bukatun cikin gida, matakin da zai rage wa masu sayayya dawainiya da kusan Yuan biliyan 1.35 a wannan shekara.
A rahoton aikin gwamnatin na wannan shekarar, kasar Sin ta yi alkawarin rage haraji da kudade masu yawa da ake biya a wannan shekara, da rage nauyi na haraji da inshorar karo-karo na kamfanoni da kusan Yuan triliyan 2.(Ibrahim)