in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC Li Zhanshu ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar dokokin kasar Burkina Faso
2019-03-27 09:45:20 cri
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC Li Zhanshu ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar dokokin kasar Burkina Faso Alassane Bala Sakandé a babban dakin taron jama'ar kasar Sin dake birnin Beijing a ranar Talata.

Li Zhanshu ya nuna yabo ga kasar Burkina Faso domin ta sake kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da kasar Sin da kuma goyon bayan da take nunawa ga ka'idar Sin daya tak.

A nasa bangare, Sakandé ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da sa kaimi ga raya dangantakar sada zumunta a tsakaninta da Sin bisa tushen ka'idar Sin daya tak, da kara yin hadin gwiwa da juna don amfanawa jama'ar kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China