Mahukuntan lardin sun ce jami'an aikin ceto, sun zakulo karin gawawwakin ma'aikata 14, bayan sun bincike wasu masana'antu 20 dake kewayen sakwaya kilomita 2, daura da kamfanin sinadaran inda fashewar ta auku.
Yayin wani taro na manema labarai da yammacin wannan rana, magajin garin Yancheng Mr. Cao Lubao, ya tabbatar da karuwar wadanda suka rasun, sakamakon wannan ibtila'i zuwa mutum 78. (Saminu Alhassan)