Yau Jumma'a 22 ga wata, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana rashin jin dadin kasarsa da kuma kin yarda da sukar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta yi wa gwamnatin kasar Sin da ma hukumar yankin musamman na Hong Kong cikin rahotonta na shekara-shekara kan manufofin Hong Kong.
Geng Shuang ya nuna cewa, tun bayan da aka maido da Hong Kong karkashin shugabancin kasar Sin, ana aiwatar da manufar "kasa daya, tsarin mulkin biyu" a Hong Kong, inda kuma mazauna yankin Hong Kong suke tafiyar da harkokinsu da kansu, kana ana kare hakkinsu da kuma 'yancinsu. Manufar gwamnatin Sin ta tafiyar da harkoki bisa kundin tsarin mulkin kasa da manyan dokokin Hong Kong da kuma bin manufar "kasa daya, tsarin mulki biyu" ba za ta sauya ba. (Tasallah Yuan)