in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibia ta yi ikirarin kawar da gibin dake tsakanin masu abin hannu da talakawa a kasar
2019-03-28 11:02:28 cri
Matsalar rashin daidaito na cigaba na yin Kamari a tsakanin al'ummar kasar Namibia ta fuskar kudaden shiga, kuma akwai bukatar kasar ta gina wata al'umma mai adalci don cike gibin dake tsakanin mawadata da matalautan kasar, ministan kudin kasar Calle Schlettwein shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Tsananin talauci ya ragu a kasar daga kaso 41 a shekarun 1990 zuwa kaso 17.4 a shekarun 2015/16, kuma a halin yanzu gibin dake tsakanin masu hannu da shuni da na 'yan rabbana ka wadatamu a kasar ya kai kashi 0.56 idan an kawatanta da kashi 0.7 a shekarun 1990s, inji Schlettwein, a lokacin da yake tattara alkaluman kasafin kudin kasar na shekarar 2019/20.

"Al'ummarmu da tsarin tattalin arzikinmu ya samu tushe ne daga tsarin tattalin arziki da siyasa na Turawan mulkin mallaka," in ji shi. "Matakin yasa har yanzu kasar Namibia ke cigaba da zama kasa ta biyu mafi fama da rashin daidaito a duniya."

"Hanya daya tilo da za mu samu nasarar samun kyakkyawar makoma ga kasarmu ita ce mu magance wannan cutar data dade tana illatamu, saboda wannann dalilin, mun zabi mu gina tsarin adalci da al'umma mai zaman daidai wa daida ta yadda dukkan al'ummar kasar Namibia za su samu damar cin gajiyar damammakin tattalin arziki da kasar ke da su," inji shi.

"Dole ne kuma mu kara samar da wasu manufofi da za su taimakawa tattalin arzikinmu wajen cike gibin dake tsakanin mawadata da talakawa da kuma yaki da kangin fatara dake addabar rayuwar al'ummarmu.'' In ji ministan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China