Karkashin shirin yiwa majalissar zartaswar kasar ta Namibia garambawul, shugaba Geingob ya dauki matakai na daidaita yawan kujerun mataimakan ministocin bisa lura da jinsinsu, kamar dai yadda wata sanarwa da ofishin fadar shugaban kasar ta bayyana.
Bisa wannan aniya dai, yanzu haka yawan mata masu rike da mukamin mataimakan ministocin kasar ya kai 17, baya ga maza 11 da ake da su. (Saminu Hassan)