Cikin wata sanarwar da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar ta bayyana cewa, ana samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar ta Maleriya a duk fadin kasar ta kudancin Afrika musamman a 'yan shekarun nan.
Sanarwar ta ce, kasar ta Namibia, ta fuskanci irin wannan matsalar tsakanin shekarar 2015 da 2018 a wasu sassan kasar.
A cewar sanarwar, an samu rahoton bullar cutar maleriya a yankunan Ohangwena, da yammacin Kavango, da Oshikoto, da kuma yankin Zambezi.
Sanarwar ta ce, ma'aikatar lafiyar kasar ta kafa wata tawagar jami'ai don yin feshin magunguna a dukkan yankunan da ake fama da cutar zazzabin maleriyar tsakanin watan Satumba zuwa tsakiyar watan Disambar 2017.
An samu nasarar gudanar da kashi 85 bisa 100 a lokacin aikin feshin, in ji sanarwar. (Ahmad Fagam)