in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude gadar zamani mafi tsawo a Afirka a Mozambique
2018-11-11 15:57:52 cri
A jiya ne aka bude gadar zamani mafi tsawo ga ababan hawa a hukumance a Mozambique. Ita dai wannan gada ta ratsa teku ne daga yankin Maputa sannan ta hadu da wasu hanyoyi a Mozambique.

Kasar Sin ce dai ta daukin nauyin aikin gina gadar ta Maputo wadda ta hade wasu hanyoyi kuma kamfanin gina hanya da gadoji na kasar Sin ne ya ginata bisa ma'aunin kasar Sin. Gadar mai tsawon kilomita uku, tana da fadin mita 680 a kan yankin Maputo dake tekun Indiya.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da gadar, shugaba Filipe Jacinto Nyusi na Mozambique, ya bayyana cewa, gadar za ta taimaka wajen saukaka zirga-zirga tsakanin kasar da yankin arewacin nahiyar Afirka, da tabbatar da fatan Afirka da aka gina yayin kafa kungiyar AU a shekarar 1963.

Shugaban ya kuma bayyana godiya ga gwamnati da al'ummar kasar Sin , bisa ga goyon bayan da suka ba da wajen samar da wannan gada da ma yadda suka kula da aikin gina gadar, yana mai cewa, Mozambique ta shiga taswirar duniya, na zama kasar da ke da gadar zamani mafi tsawo a Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China