in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda ya bukaci kasashen gabashin Afirka da su rika sayan kayayyakin da aka sarrafa a shiyyar
2019-03-28 10:26:08 cri
Shugaba Yoweri Museveni na Uganda, ya yi kira ga kasashen gabashin Afirka, da su rika sayan kayayyakin da aka sarrafa a shiyyar, domin rage shigo da kayayyakin da ake iya sarrafa wa a yankin.

Museveni, wanda ke ziyarar aiki ta yini biyu a kasar Kenya, ya bayyana cewa, kasashen shiyyar na hasarar miliyoyin daloli daga kayayyakin da ake shigo da su, duba da yadda manyan kamfanonin dake gabashin nahiyar suka lalace.

Don haka, ya yi kira ga kasar Kenya, da ta hanzarta farfado da masana'antar samar da takarda ta Webuye wadda ke da muhimmanci wajen samar da kayayyakin takardu a gabashin Afirka.

Shugaban Museveni ya ce, darajar takaradun da kasarsa ke shigo da su daga Finland ta kai dala miliyan 130, kwatankwacin kudin kasar Shilling biliyan 13, amma har yanzu masana'antar sarrafa takardu dake kasar Kenya ba ta aiki.

Ya yi nuni da cewa, karfafa matakan kula da manyan kwantenonin kaya a tashar ruwa da ma yadda ake zirga-zirgar kayayyaki tsakanin yankin arewacin nahiyar, suna da matukar tasiri ga tattalin arzikin kasashen Kenya da Uganda, da ma sauran kasashen da suka dogara da tashar ruwa ta Momabasa, wajen harkokinsu na shige da fice, ciki har da kasasahen Rwanda, da Burundi, da Sudan ta kudu da Jamhuriyar Demokiradiyar Congo.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China