in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uwargidan shugaban kasar Sin ta halarci taron UNESCO kan ilimin mata da 'yan mata
2019-03-27 09:41:54 cri

Peng Liyuan, Uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta halarci wani taron musamman kan ilimin mata da 'yan mata da hukumar bunkasa ilimi kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO ta shirya a hedkwatar hukumar.

Yayin taron da aka yi jiya, wasu daga cikin wadanda suka samu lambar yabo ta UNESCO, saboda gudumawar da suka bayar ga ci gaban ilimin mata, sun gabatar da takaitattun jawabai game da fahimtarsu da kuma inganta ilimin mata.

Peng Liyuan, wadda wakiliya ce ta musamman ta UNESCO kan karfafa ilimin mata, ta yaba da kokarin da UNESCO da wadanda aka karrama suka yi, tare da bayyana musu nasarorin da kasar Sin ta cimma a wannan fanni. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China