in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Faransa za su hada gwiwa don kyautata harkokin kasa da kasa
2019-03-27 09:40:08 cri

Kasashen Sin da Faransa sun yi alkawarin yin hadin gwiwa domin kare manufar cudanyar kasashen duniya, da inganta yadda ake tafiyar da harkokin kasa da kasa, kamar yadda kasashen biyu suka bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwa a ranar Talata a yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ci gaba da gudanarwa a kasashen Turai.

Kasashen biyu sun yi amanna cewa, a halin da ake ciki yanzu, tabbatar da manufar cudanyar kasashen duniya shi ne hanya daya mafi inganci wajen daga matsayin hadin gwiwar kasa da kasa domin dakile dukkan barazana da manyan kalubalolin dake addabar zaman lafiya da ci gaba duniya, in ji sanarwar hadin gwiwar.

Game da batun tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya kuwa, kasashen biyu sun bukaci a mayar da tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya bisa tsarin bude kofa, ba tare da rufa rufa ba, da yin cudanya da juna kuma ba tare da nuna wariya ba, da kiyaye ka'idojin kungiyar WTO bisa tushen mutunta dokokin cinikayya na gamayyar kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China