Shugaba Xi Jinping, ya ce shekaru 55 da suka gabata, a wani karsashi na murnar samun 'yanci, General Charles de Gaulle, ya yanke muhimmiyar shawarar kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin.
Ya kara da cewa, irin wannan karsashi ya kara zama mai muhimmanci matuka, a lokacin da duniya ke fuskantar sauye-sauyen da ba a taba gani ba a cikin karni.
A nasa bangaren, Richard Ferrand ya ce a shirye Faransa take ta hada hannu da kasar Sin wajen kare tsarin huldar kasa da kasa da karfafa dangantaka tsakanin Tarayyar Turai da kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)