in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Jamus sun yi alkawarin daga matsayin dangantakarsu zuwa mataki na gaba
2017-07-06 10:01:56 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun yi alkawarin daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasashensu zuwa wani sabon mataki.

Jagororin kasashen biyu sun bayyana hakan ne, yayin da suke tattaunawa game da sabbin matakan da suka dauka na bunkasa hadin gwiwar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.

Shugaba Xi ya bayyana a yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu cewa, a shirye kasar Sin take ta hada kai da Jamus a fannin mutunta juna da kara cimma daidaito da bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Xi ya kuma yi kira ga bangaren Jamus da ya karfafa musayar jami'ai, ta yadda za su rika musayar ra'ayoyi da karfafa fahimtar juna a fannin harkokin siyasa da amincewa da juna.

A nata bangare, Madam Merkel ta ce, ta karanta sharhin da shugaba Xi ya rubuta wanda aka wallafa a jaridar Die Welt ta kasar Jamus, kuma ta yarda cewa, hadin gwiwar Jamus da Sin a fannonin siyasa, tattalin arziki, da al'adu, da musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu, ta dace da muradun sassan biyu, kana za ta kara haifar da sakamako mai kyau.

Bugu da kari, shugabannin biyu, sun kalli yadda aka sanya hannu a kan jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa, kama daga masana'antu ya zuwa fasahar yanar gizo da fasahohin zamani da bincike kan dabbar Panda, daga bisa kuma suka gana da manema labarai.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China