Shugaba Xi Jinping na kasar Sin wanda ke ziyara a kasar Jamus, ya bayyana cewa, kasashen Sin da Jamus sun shiga wani sabon karni a dangankatar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier. Ya ce, a shirye kasar Sin take ta hada kai da Jamus don ganin ta karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za ta amfani al'ummomin kasashun biyu, su kuma hada kai don tabbatar da zaman lafiya da makoma mai kyau a duniya.
A nasa jawabin, Mr Steinmeier, ya ce, ita ma Jamus a shirye take ta hada kai da kasar Sin don karfafa hadin gwiwar kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar G20, da ba da gudummawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.(Ibrahim)