Lu ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Juma'a, inda ya ce, kudurin ya dace da muradun jama'ar Burkina Faso, kuma ya nuna cewa, kasashen duniya na martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya. Baya ga haka, Lu ya ce, kasar Sin na son gudanar da hadin kai irin na samun moriyar juna bisa tushen girmama juna da zaman daidaiwa daida tare da duk kasashen dake zumunta da ita.(Bilkisu)