in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an kamfanonin Afirka sun gana da juna domin tattauna manyan batutuwan sassa masu zaman kan su
2019-03-25 20:00:10 cri
Kimanin manyan jami'an kamfanonin nahiyar Afirka, da masu zuba jari na kasa da kasa, da kwararru, da manyan masu tsara manufofi 1,500 ne suka taru a birnin Kigalin kasar Rwanda, domin gudanar da wani taron nazartar manyan batutuwa, da kalubale dake addabar sassa masu zaman kan su.

An dai bude taron ne a yau Litinin, inda ake sa ran tattauna batutuwa da suka jibanci cinikayya, da zuba jari tsakanin kasashen Afirka, da batun samar da karin kariya ga manufofin nahiyar da masana'antun ta, da ingiza ci gaban sassa masu zaman kan su ta fannin samar da ababen more rayuwa da zirga zirga, da tsara tarukan karawa juna sani, da bincike game da hadin gwiwar kamfanonin hukuma da masu zaman kan su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China