in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda ta zargi Afrika ta Kudu da yunkurin haddasa jinkiri a shirin farfadowar dangantaka a tsakaninsu
2018-12-13 09:55:52 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rwanda ta sanar a jiya Laraba cewa kasar Afrika ta kudu tana yunkurin haifar da jinkiri ko kuma yin kafar ungulu game da shirin farfado da dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rwandan ce ta sanar da hakan.

Batutuwan sun hada da "zarge zarge marasa tushe" wadanda ake yi wa kasar Rwanda a bainar jama'a ko kuma a kafafen yada labarai, bisa ga jita-jita da kalaman batancin da masu neman zubarwa Rwandan mutuncinta ke yi, wadanda suke zaune a kasashen Canada da Afrika ta Kudu, da kuma kafafen yada labarai dake da alaka da su.

Rwanda da Afrika ta Kudu sun fara fuskantar tsamin dangantaka ne tun bayan da kasar Afrika ta Kudu ta kori wasu jami'an diplomasiyyar kasar Rwandan su 3 a shekarar 2014, wadanda ta danganta su da yunkurin afkawa gidan wani janar din soja kasar Rwandan dake gudun hijira a Johannesburg, inda kasar Rwandan ta mayar da martani ta hanyar korar wasu jami'an diploamsiyyar Afrika ta Kudu su 6.

Ministan harkokin wajen Rwandan Richard Sezibera, ya sanar a watan Nuwamba cewa tuni shugabannin kasashen Rwanda da Afrika ta Kudu suka umarci ministocin harkokin wajen kasashen biyu da su tattauna game da lalubo hanyoyin farfado da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China