in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Rwanda sun ceto fararen hula 74 wadanda mahara suka yi garkuwa dasu
2018-12-19 11:41:24 cri
Dakarun tsaron kasar Rwanda (RDF) sun yi nasarar kubutar da fararen hula kimanin 74 wadanda aka yi garkuwa da su a ranar Asabar lokacin wani hari da aka kaddamar a yankin Nyamagabe dake kudancin kasar Rwanda.

Dakarun tsaron sun fara gudanar da aikinsu ne tun bayan samun rahoton kaddamar da harin, kakakin rundunar sojojin kasar Innocent Munyengango, shine ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Xinhua a zantawarsu ta wayar tarho.

Maharan wadanda ba'a gano ko su wane ne ba, sun tsare wasu motocin fasinja 3 da yammacin ranar Asabar a kusa da Nyamagabe dake kan iyakar kasar da Burundi, inda suka hallaka mutane 2 da jikkata wasu mutanen 8, sojojin sun tabbatar da hakan ne da yammacin ranar Asabar.

Yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 4 bayan da wasu mutum biyu suka mutu daga cikin wadanda suka jikkata, sojojin Rwandan sun bayyana a ranar Litinin cewa, suna cigaba da zakulo wadanda ke da hannu, amma sun yi nasarar hallaka maharan 3 yayin da ragowar suka tsere zuwa kasar Burundi.

Sai dai dakarun sojojin sunce ya zuwa yanzu, akwai cikakken tsaro a yankin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China