in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda da Alibaba na tattauna yadda za su kara fitar da kayan amfanin gona zuwa kasar Sin
2019-01-07 10:41:49 cri
A jiya ne hukumar raya kasa ta Rwanda(RDB) ta gana da wata tawagar katafaren kamfanin cinikayya ta yanar gizo na Alibaba na kasar Sin, a Kigali babban birnin kasar, domin tattauna yadda za a kara fitar da kayayyakin amfanin gonan kasar zuwa kasar Sin.

Da take karin haske, shugabar hukumar ta RDB Claire Akamanzi ta ce, kasar Sin ta samarwa Rwanda babbar kasuwa, kana kasa mai yawan al'umma baya ga karuwar kudaden da ake kashewa. Tana mai cewa, hukumarta za ta yi amfani da kyakkyawar damar da kasuwar kasar Sin ke da ita.

Sassan biyu dai na son taimakawa kamfanonin kasar Rwanda wajen fitar da karin kayayyakin amfanin gona kamar naman shanu, avocado, barkono, wake, tumatur da sauran kayayyakin lambu da ganyaye zuwa kasar Sin, ta hanyar samar da muhimman kayayyakin more rayuwa da za su bunkasa yadda ake sarrafa kayayyakin amfanin gona, da rage kudin da ake kashewa wajen jigilarsu ta jiragen sama, da kara samar da horo ga 'yan kasuwan kasar Rwanda ta yadda za su kara yawan kayayyakin da suke fitarwa da ma sauran hanyoyi.

Sanya hannu kan wannan yarjejeniya tsakanin sassan biyu, ya sanya kasar Rwanda zama ta farko a nahiyar Afirka da ta kaddamar da tsarin cinikayya ta yanar gizo wato eWTP a takaice, tsarin da shugaban kamfanin na Alibaba, Jack Ma ya gabatar da nufin bunkasa tattaunawa tsakanin gwamnati da sassa masu zaman kansu, domin kara karfafa da ma inganta tsari da yanayin kasuwanci da zai baiwa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa damar shiga a dama da su a harkokin cinikayyar yanar gizo tsakanin kasashe.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China