in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Italiya sun gana da 'yan kasuwa da masu aikin al'adu na kasashen 2
2019-03-23 16:20:58 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Italiya Sergio Mattarella sun gana da wakilan kasashen 2, wadanda suka halarci wasu tarukan 'yan kasuwa da masu aikin al'adu.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana son hada kai da rukunoni daban daban na Italiya wajen kara azama kan ganin kasashen 2 sun samu moriyar juna da nasara, da kuma ba da sabuwar gudummawa wajen sa kaimi ga hadin kan kasashen Sin da Turai da ma ci gaba da wadatuwar duniya. Shugaba Xi Ya yi fatan cewa, 'yan kasuwa da masu aikin al'adu na Sin da Italiya, za su kara nuna hazaka da kokari a fannoninsu domin inganta hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2.

Shugaba Mattarella ya ce, dole ne Italiya da Sin su hada hannu wajen daga matsayin hadin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki da habaka hadin gwiwarsu ta fuskar al'adu da kara amfanawa jama'arsu da daidaita kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta yanzu da bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa sabon matsayi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China