Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana kwamandan askarawar kasar, ya ba da wannan umarni ne yayin da yake rangadin aiki a kasashen wajen.
Shugaba Xi ya ce, wajibi ne a dauki dukkan matakai na ganin an gano wadanda suka makale, kana a yiwa wadanda suka jikkata magani a kan lokaci, haka kuma wajibi ne a gudanar da aikin ceto yadda ya kamata don ceton rayukan jama'a.
A halin da ake ciki kuma, ya kamata a inganta yanayin sanya-ido da matakan gargadi domin kare gurbatar muhalli da aukuwar manyan bala'u.
Hukumomin yankin sun bayyana cewa, fashewar ta faru ne da misalin karfe 2 da mituna 48 na ranar Alhamis agogon wurin , bayan da wata gobara ta tashi a dakin adana sinadarai dake rukunin masana'antar, lamarin da ya haddasa jikkata da hasarar rayuka. (Ibrahim)