in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya fara ziyara a kasar Italiya
2019-03-22 10:19:21 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa filin jiragen sama na Fiumicino dake birnin Rome na kasar Italiya a maraicen jiya.

A cikin jawabinsa da ya yi a filin jiragen saman, Xi Jinping ya yi bayani game da mu'amalar dake tsakanin Sin da Italiya, da nasarorin da aka samu na bunkasuwar hadin gwiwa bayan da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu.

Xi Jinping yana fatan yin shawarwari tare da shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella da firaministan kasar Giuseppe Conte da sauran shugabannin kasar don tattauna shirin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba.

Ziyarar Xi Jinping a nahiyar Turai ta jawo hankali sosai.

Shekarar bana shekara ce da cika shekaru 15 da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da Italiya. Kasar Italiya ta kasance zango na farko na ziyarar Xi a nahiyar Turai a wannan karo, kuma ita ce ziyara ta farko da shugaba Xi ya kai a kasashen waje a shekarar 2019. Manazarta suna ganin cewa, shugaba Xi ya zabi kasashe uku na Turai a matsayin kasashen farko da ya kai ziyara a bana, hakan ya shaida cewa Sin ta maida hankali sosai ga dangantakar dake tsakanin Sin da Turai, kana birnin Rome ya zama wuri na farko da shugaba Xi ya kai ziyarar, wanda ya kara jawo hankalin duniya sosai.

Ana sa ran cewa, raya shawarar "ziri daya da hanya daya" zai kasance daya daga cikin manyan batutuwan da za a tattauna a yayin ziyarar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China