Yayin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ke ziyarar aiki a kasar Italiya, jiya Alhamis, kamfanonin yada labaru na Mediaset da Class Editori mafiya tasiri a Italiya sun fara nuna shirin bidiyo mai taken "Bayanan magabata da Xi Jinping ke sha'awar karantawa" na harshen Italiyanci a gidan telabijin, wayar salula da shafin Intanet.
Wannan shirin bidiyo da babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya kaddamar ya samu amincewa sosai daga mazauna wurin.
Attilio Massimo Iannucci, tsohon jakadan Italiya a kasar Sin ya bayyana yayin da yake zantawa da manema labaru cewa, wannan shirin bidiyo ya bai wa jama'ar Italiya wata damar kara fahimtar tunanin shugaba Xi Jinping kan mulkin kasa. Wasu shahararrun jimlolin da shugaba Xi ya ambato sun bayyana bukatun kasar Sin na samun ci gaba a sabon zamani.
Francesco Boggio Ferraris, shugaban makarantar ba da horo na asusun Italiya da Sin ya bayyana wa manema labaru cewa, shugaba Xi Jinping ya san al'adun gargajiyar kasar Sin sosai. Yana amfani da kyawawan fasahohin tarihi cikin tunaninsa na tafiyar da harkokin kasa a sabon zamani. (Tasallah Yuan)