in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya isa Italiya domin fara ziyarar aiki
2019-03-22 09:09:55 cri

A jiya Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa kasar Italiya domin fara ziyarar aiki, wadda za ta ba da zarafin karfafa alakar kasashen biyu, da kuma daga matsayin ta zuwa wani sabon mataki. Ziyarar dai ita ce irin ta ta farko da wani shugaban kasar Sin ya kai Italiya cikin shekaru 10.

Wasu jiragen yakin kasar biyu sun raka jirgin shugaba Xi, yayin da ya shiga sararin samaniyar kasar. Shugaban tare da mai dakin sa Peng Liyuan, sun samu tarba daga filin jirgin saman kasar daga manyan kusoshin gwamnatin Italiya.

Da yake jawabi jim kadan da saukar sa, shugaba Xi ya ce alakar Sin da Italiya ta shafe tsawon lokaci cikin aminci duk kuwa da sauye sauye da aka gamu da su a matakai na kasa da kasa, inda kasashen suka shafe shekaru 49 suna cudanya mai nagarta.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, yana fatan zama tare da jagororin kasar Italiya, domin tsara manufar ci gaban sassan biyu a nan gaba.

Kasar Italiya ce zangon farko a ziyarar da shugaba Xi zai gudana a kasashen Turai uku, inda ake sa ran nan gaba zai ziyarci Monaco da kuma kasar Faransa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China