A cikin sakonsa, shugaban kasar Sin ya ce, mahaukaciyar guguwa ta Idai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu da haddasa asarar dukiyoyi a kasashen Mozambique, Zimbabwe da Malawi. A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar, da kuma shi kansa, shugaba Xi ya nuna damuwarsa kan wannan bala'i, kana ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka bace, da wadanda suka ji rauni, da ma wadanda bala'in ya rutsa da su. Yanzu jama'ar kasashen 3 suna fama da radadin wannan bala'in. Kasar Sin ta fahimci kuncin da suke ciki sosai. Ya yi imanin cewa, a karkashin shugabancin gwamnatocin kasashen 3, jama'arsu za su jure kuncin bala'in, za su kuma sake gina gidajensu cikin sauri. (Tasallah Yuan)