in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai yuwuwar kasashen Sin da Kenya za su cimma yarjejeniyoyi da dama
2019-03-20 14:21:35 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya, ya shirya taron manema labaru a jiya Talata, inda mukaddashin jakadan kasar Sin, Li Xuhang ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta gayyaci manyan shugabannin kasar Kenya don halartar taron koli da za a gudanar a karo na biyu na dandalin tattaunawa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya".

A yayin taron manema labaru da aka shirya a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya, mukaddashin Jakada Li Xuhang ya yi bayani ga jami'ai da kwararru masu bada shawarwari ko yin bincike da manema labaru na kasar ta Kenya, game da "taruka biyu" na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) da majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar(CPPCC), da taron koli na dandalin tattaunawa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" da za a gudanar a karo na biyu, da kuma hanyar dogo ta Mombasa-Nairobi. Li ya bayyana cewa, kasar Sin ta kara ba da tabbaci kan inganta bude kofa ga kasashen ketare a dukkan fannoni a yayin "taruka biyu". Kana Kasar Sin, kasa ce da ta fi ba da gudummowa kan ci gaban tattalin arzikin duniya, inda yawan gudummowar ya wuce kashi 30 cikin dari a cikin 'yan shekarun da suka wuce a jere. An yi hasashen cewa, a cikin shekaru 15 masu zuwa, yawan darajar kayayyaki da hidimar da kasar Sin za ta shigo da su daga ketare, zai wuce dalar Amurka triliyn 30 da triliyn 10. Li ya ce,

"Kara bude kofa ga kasashen ketare da neman bunkasuwa da kasar Sin ke yi, zai kara samar da damar hadin kai ga kasar Kenya, kana kasuwar kasar Sin dake dada habaka za ta kara samar da dama ga kasar Kenya wajen fitar da kayayyakinta."

Game da batun taron koli na dandalin tattaunawa kan shawarar "Ziri daya da hanya daya" karo na biyu da za a shirya a karshen watan Afrilu a nan birnin Beijing, Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru 6 da suka gabata da aka gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", shawarar ta riga ta kasance wani dandalin hadin kai mafi girma a duniya. Ya zuwa yanzu, akwai kasashe 123 da kungiyoyin kasa da kasa guda 29 da suka sa hannu kan takardun hadin kai na inganta shawarar "Ziri daya da hanya daya", kuma dukkansu sun jefa kuri'unsu na amincewa da goyon bayan shawarar. Li ya ce,

"Kasashen Afirka, ciki har da kasar Kenya su ne muhimman kasashe wajen shiga shawarar 'Ziri daya da hanya daya', ya zuwa lokacin taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka da aka shirya a bara a Beijing, kasar Sin ta riga ta sanya hannu kan takardar fahimtar juna game da shawarar tsakaninta da gwamnatocin kasashen Afirka 37 da kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU. Kasar Kenya ta ba da jagoranci ta kuma zama abin koyi wajen hadin gwiwar Sin da Afirka kan raya shawarar. Kasar Sin ta riga ta gayyaci manyan shugabannin kasar Kenya don halartar taron koli na dandalin tattaunawa game da shawarar 'Ziri daya da hanya daya' karo na biyu. A yayin taron kolin kuma, akwai yuwuwar bangarorin biyu za su cimma yarjejeniyoyi da dama a fannonin kara fitar da kayayyakin aikin gona na Kenya zuwa kasar Sin da zuba jari kan manyan kayayyakin more rayuwa da gina birane na zamani da kuma ba da horo a bangaren da ya shafi ayyukan hanyar dogo da dai sauransu."

A matsayinta na muhimmiyar nasara da aka cimma sakamakon shawarar "Ziri daya da hanya daya", hanyar dogo ta Mombasa-Nairobi ta soma cimma nasara bayan shekara guda da ta fara aiki. Ban da wannan kuma, yanzu kamfanin CCCC na kasar Sin na gudanar da aikin gina hanyar dogo ta Nairobi-Malaba, wanda ya kasance aikin dake iya alamanta muradun kasar Kenya kafin shekarar 2030. Hanyar dogon ta dora ne daga inda hanyar Mombasa-Nairobi ta tsaya, har zuwa arewa maso yammacin kasar Kenya. Inda ake sa ran za ta hade da wasu kasashen gabashin Afirka, ciki har da Uganda, Sudan ta kudu, Rwanda da dai sauransu, wanda hakan zai karfafa dunkulewar gabashin Afirka.

Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin Asiya da Australia na ma'aikatar harkokin wajen kasar Kenya Lindsay Kiptiness ya bayyana cewa, kasarsa ta yabawa rawar da kasar Sin ke takawa kan batun cinikayyarta. Ya kara da cewa, ya na sa ido kan taron koli na dandalin tattaunawa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" da za a shirya a watan Aflilu. 

"A gani na, gina hanyar dogo ta Nairobi-Malaba ba aiki ne na Kenya kadai ba. Muna sa ran ganin, hanyar dogon ta isa cikin Uganda, har da danganawa da tekun Atlantika. A lokacin, kasar Kenya za ta kasance hanyar dake hada Asiya ko Sin da tekun Atlantika da kudancin nahiyar Amurka." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China