in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin dake Kenya ya kira liyafar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sin
2019-01-27 17:18:48 cri

Jiya Asabar da dare, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya ya kira liyafar taya murnar sabuwar shekarar 2019 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya. Mutane sama da 300 sun halarci liyafar, wadanda suka hada da sinawa dake kasar Kenya, wakilan kamfanonin Sin dake kasar, da wasu malamai da dalibai na kwalejin Confucius.

A yayin liyafar, mukaddashin jakada na wucin gadi na kasar Sin dake kasar Kenya Li Xuhang ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Kenya, cikin shekaru 55 da suka gabata, kasashen biyu suna ci gaba da zurfafa dangantakar dake tsakaninsu, kana hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu ya riga ya kasance abin koyi ga sauran kasashen Afirka. Cikin shekarar 2018 da ta wuce, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya kai ziyarar aiki sau biyu a kasar Sin, inda shugabannin kasashen biyu suka cimma nasarar tsara hanyar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba. haka kuma, shugaba Kenyatta ya nuna yabo matuka kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasarsa, ya kuma musanta zargin da ake yiwa kasar Sin cewar, Sin ta shiga kasashen Afirka don jefa su cikin "tarkon bashi".

Ya zuwa yanzu, jiragen kasa dake kan layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi sun riga sun yi jigilar fasinjoji kimanin miliyan 2.3 lami lafiya, da kuma kayayyaki sama da ton miliyan 3. Kana, adadin Sinawa da suka je yawon shakatawa a kasar Kenya ya wuce dubu 80. Lamarin da ya nuna cewa, lalle an cimma sakamako masu kyau da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya a bisa fannoni dabban daban. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China