Bisa ga daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a kasar Argentina, sassan biyu sun tattauna batutuwan da suka jawo hankalin kasar Sin, ciki har da daidaita ciniki da musayar fasahohi da kariyar hakkin mallakar ilmi, da shingayen ciniki da ba na kudin kwastan ba, da aikin gona da sauransu, inda suka samu muhimmin sakamako. Ban da haka, sassan biyu sun kuma tabbatar da lokacin da za a gudanar da shawarwari na gaba.
Sassan biyu sun maida matukar muhimmanci a kan batun kare hakkin mallakar ilmi da musayar fasahohi, kuma sun amince da kara inganta hadin gwiwa a tsakaninsu. Samar da yanayin kasuwanci mai adalci ya dace da manufar kasar Sin ta bude kofa, don haka, kasar Sin zata maida hankali kan kulawar da kasar Amurka ta nuna.
Baya ga haka, bangarorin biyu sun kuma amince da daukar matakai na inganta daidaiton ciniki a tsakaninsu. Kasar Sin zata kara shigo da amfanin gona da kayayyakin makamashi da na masana'antu da hidimomi daga kasar ta Amurka, don biyan bukatunta na kara samun ingancin ci gaban tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar jama'a. (Lubabatu)