in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lokacin sake yin shawarwari kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka na da nasaba da ra'ayin Amurka
2018-09-25 13:55:33 cri
Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin, kuma mataimakin wakilin ma'aikatar kasuwancin Sin mai kula da shawarwari kan ciniki a tsakanin kasa da kasa Wang Shouwen, ya bayyana a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, lokacin sake yin shawarwari kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, yana da nasaba da ra'ayin Amurka.

Wang Shouwen ya ce, yanzu Amurka ta dauki matakan kayyade ciniki tsakaninta da Sin, hakan ya haddasa rashin daidaito a shawarwarin. Kana an riga an yi shawarwari a tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka har zagaye hudu, inda aka cimma ra'ayi bai daya a fannoni da dama, har ma bangarorin biyu sun fitar da hadaddiyar sanarwa, amma Amurka ta sabawa alkawarinta, inda ta dauki matakan kayyade ciniki dake tsakaninsu, don haka ba za a iya ci gaba da shawarwarin ba.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China