Yayin taron manema labarai da aka saba yi a kullum, kakakin ma'aikatar Geng Shuang, ya ce Amurka ce ke kan gaba ta fannin karfin fasaha a duniya, sai dai bai kamata kasar ta mayar da hankali ga ci gabanta kadai ta hanawa ci gaban sauran kasashe ba.
Wannan tsokaci na zuwa ne bayan mataimakin shugaban kwamitin tattara bayanan sirri na majalisar dattawan kasar Amurka, Mark Warner da shugaban marasa rinjaye na majalisar, Charles Schumer, suka zargi Sin da saci fasahar kasarsu.
Har ila yau, Geng Shuang, ya ce bai dace Amurka ta rika suka da zargin ci gaban fasahar sauran kasashe ba. (Fa'iza Mustapha)