Jawabin ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen biyu ya samar da nasara ga juna tsakanin kasashen biyu, kana hakan ya taimaka wajen kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya. Jawabin ya kuma kara da cewa, moriyar bai daya ta wuce sabani dake tsakanin kasashen biyu, kuma hadin gwiwa da juna shi ne zabi daya kacal gare su.
Ya ce a sabon yanayin da ake ciki, kasashen biyu suna fuskantar rashin tabbas a huldarsu, kuma idan an hangi shekaru 40 masu zuwa, ya kamata jama'ar kasashen biyu su tabbatar da makomar huldar kasashen na su.