in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda kasar Sin take kare hakkin dan Adam, nasarori da aniyarta sun samu amincewar duniya
2019-03-18 20:35:17 cri

Yau Litinin 18 ga wata, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi wa manema labaru bayanin cewa, kwanan baya, kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ya yi nazari da kuma amincewa da rahoton kasar Sin kan kare hakkin dan Adam karo na 3. Kana kuma Le Yucheng, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi karin bayani kan muhimmin ci gaban da kasar Sin ta samu wajen daukar sabbin matakai guda 30 na kare hakkin dan Adam. Hanyar da kasar Sin take bi wajen kare hakkin dan Adam, nasarorin da ta samu a wannan fanni da kuma aniyarta sun samu amincewar kasa da kasa.

Rahotanni na cewa, kwanan baya Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana a yayin taron kaddamar da rahoton kasa da kasa kan kare hakkin dan Adam cewa, kasar Sin ta fi kowa ce kasa keta hakkin dan Adam a duniya. Dangane da wannan batu, Geng Shuang ya ce, kasar Sin ta yi watsi da zargi maras tushe da Amurka ta yi mata. Ta kuma tuntubi Amurka a hukumance. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China